30 Yuli 2024 - 19:31
An Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Iran

Dr. Mas'ud Pezeshkian ya karanta rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa

Dr. Mas'ud Pezeshkian ya karanta rantsuwar shugaban kasa a babban taron al'umma na ciki da wajen kasar Iran a yau.

Kamfanin Dillancin Labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (AS) - ABNA- ya habarta maku cewa: Dr. Mas'ud Pezeshkian, sabon zaɓaɓɓen shugaban kasar Iran ya biya rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban jamhuriyar Iran na 9, inda ya karanta rantsuwar shugabancinsa a dinbin taron jama'a a yau (Talata, 30 ga watan Yuli 2024) bisa dogaro da faɗar doka ta 121 na Kundin Tsarin Mulkin Kasar Iran.

Ga bayanin rantsuwar shugaban kamar haka:

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai

“A matsayina na shugaban kasa, ina rantsuwa da Allah Madaukakin Sarki a gaban kur’ani mai tsarki da al’ummar Iran cewa zan zamo mai biyayya ga addini da tsarin tsarin Jamhuriyar Musulunci, kuma zan yi amfani da dukkan basirata, cancanta ta hanyar sauke nauyin da na dauka da sadaukar da kai wajen yi wa al’umma hidima da daukaka kasa, inganta addini da dabi’u, goyon bayan gaskiya da shimfiɗa adalci, da nisantar duk wani nau’in mulkin kama-karya, tare da goyon bayan ‘yanci da walwala da mutuncin daidaikun mutane da hakkokin da kundin tsarin mulkin kasa ya tanada. Ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen kare iyakoki da ‘yancin kai na siyasa, tattalin arziki da al’adun kasa ba, kuma da taimakon Allah da biyayya ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da A'immah Tsarkaka, ikon da al’umma ta ba ni amana mai tsarki zan kiyaye shi kamar yadda amintacce mai rikon amana ya ke kuma in bayar da ita ga wanda al’umma suka zaba a bayana”.

Kamar yadda sashi na 121 na kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, zababben shugaban kasar ya karanta rantsuwar sa tare da sanya hannu kan takardar a taron da ya gudana a gaban shugaban ma’aikatan shari’a da ‘yan majalisar masu tsaron juyin juya halin Musulunci.

....................